Amma da lokacin tashinmu ya yi, muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu, dukansu kuma har da matansu da 'ya'yansu, suka raka mu bayan gari, sa'an nan muka durƙusa a kan gaci, muka yi addu'a, muka yi bankwana da juna.
Sa'ad da Daniyel ya sani an sa hannu a dokar, sai ya tafi gidansa. Ya buɗe tagogin benensa waɗanda suke fuskantar Urushalima. Sau uku kowace rana yakan durƙusa ya yi addu'a, yana gode wa Allahnsa kamar yadda ya saba.
Sulemanu ya riga ya yi dakali na tagulla, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, tsayinsa kamu uku, ya ajiye shi a tsakiyar filin, ya tsaya a kai. Ya durƙusa a gwiwoyinsa, a idon dukan taron jama'ar Isra'ila, ya ɗaga hannuwansa sama,
Amma Bitrus ya fitar da su duka waje, ya durƙusa, ya yi addu'a. Ya juya wajen gawar, ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe ido, da ta ga Bitrus, ta tashi zaune.
Na zamar muku abin misali ta kowace hanya, cewa ta wahalar aiki haka lalle ne a taimaki masu ƙaramin ƙarfi, kuna kuma tunawa da Maganar Ubangiji Yesu da ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”