sai dai kamar yadda Allah ya yarda da mu, ya damƙa mana amanar bishara, haka muke sanar da ita, ba domin mu faranta wa mutane rai ba, sai dai domin mu faranta wa Allah, shi da yake jarraba zukatanmu.
Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafunci, ko makirci, ko yi wa Maganar Allah algus, amma ta wurin bayyana gaskiya a fili, sai kowane mutum ya shaidi gaskiyarmu a lamirinsa a gaban Allah.
A cikinsa ne aka maishe mu abin gādo na Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukkan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi,
Na zamar muku abin misali ta kowace hanya, cewa ta wahalar aiki haka lalle ne a taimaki masu ƙaramin ƙarfi, kuna kuma tunawa da Maganar Ubangiji Yesu da ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”
Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana.
Ban riƙe labarin cetonka don kaina kaɗai ba, Nakan yi maganar amincinka, da taimakonka a koyaushe. Ba na yin shiru a taron dukan jama'arka, Amma ina ta shaida madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.
“Ka tsaya a filin Haikalin Ubangiji, ka yi wa dukan biranen Yahuza magana, su waɗanda suka zo Haikalin Ubangiji domin su yi sujada. Ka faɗa musu dukan maganar da na umarce ka, kada ka rage ko ɗaya.
Sai mutumin nan ya ce mini, “Ɗan mutum ka duba da idonka, ka ji da kunnuwanka, ka kuma mai da hankali ga dukan abin da zan nuna maka, gama saboda haka aka kawo ka nan. Sai ka sanar wa jama'ar Isra'ila abin da ka gani duka.”
Babu wata kalmar da Musa ya umarta, da Joshuwa bai karanta a gaban dukan taron Isra'ilawa ba, tare da mata da ƙanana, da baƙin da suke zaune tare da su.