14 Da ya same mu a Asus, muka ɗauke shi a jirgin, muka zo Mitilini.
14 Da ya same mu a Assos, sai muka ɗauke shi a jirgin ruwan muka zo Mitilen.
Mu kuwa muka yi gaba zuwa jirgin, muka miƙe sai Asus da nufin ɗaukar Bulus daga can, don dā ma haka ya shirya, shi kuwa ya yi niyyar bi ta ƙasa.
Daga nan kuma muna tafe a jirgin ruwan dai, kashegari kuma sai ga mu daura da tsibirin Kiyos. Kashegari kuma, ga mu a tsibirin Samas, kashegari kuma sai Militas.