Ayyukan Manzanni 2:4 - Littafi Mai Tsarki4 Sai duk, aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka kuma fara magana da waɗansu harsuna dabam dabam, gwargwadon yadda Ruhun ya yi musu baiwar yin magana. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka ina cike da fushin Ubangiji Na gaji da kannewa. Ubangiji ya ce, “Zan kwararo fushi kan yara da suke a titi. Da kuma kan tattaruwar samari. Za a ɗauke mata da miji duka biyu, Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufa tukub-tukub. Za a ba waɗansu gidajensu, da gonakinsu, da matansu, Gama zan nuna ikona in hukunta mazaunan ƙasar.