'Ya'ya maza na waɗanda suka zalunce ki za su zo, Su rusuna, su nuna bangirma. Dukan waɗanda suka raina ki za su yi sujada a ƙafafunki. Za su ce da ke, ‘Birnin Ubangiji,’ ‘Sihiyona, Birni na Allah Mai Tsarki na Isra'ila.’
Bisa ga ayyukansu, haka zai sāka musu hasala, a kan maƙiyansa kuwa ramawa, a kan abokan gābansa, zai rama, da kuma a kan ƙasashen da suke a bakin gāɓa.
Sarakuna za su zama kamar iyaye a gare ku, Sarauniyoyi za su yi renonku kamar uwaye. Za su rusuna har ƙasa su ba ku girma, Da tawali'u za su nuna muku bangirma. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji, Dukan mai jiran taimakon Ubangiji, ransa ba zai ɓaci ba.”