Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 2:23 - Littafi Mai Tsarki

23 shi Yesun nan fa, an ba da shi bisa ƙaddarar Allah da rigyasaninsa, ku kuwa kuka gicciye shi, kuka kashe shi, ta hannun masu zunubi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 2:23
39 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Lalle Ɗan Mutum zai ƙaura kamar yadda aka ƙaddara, duk da haka, kaiton mutumin nan da yake ba da shi!”


Sun haɗa kai domin su yi dukan abin da ka ƙaddara zai auku, bisa ga ikonka da nufinka.


Amma ta haka Allah ya cika faɗar da ya riga ya yi ta bakin annabawa duka, cewa Almasihunsa zai sha wuya.


A nufinku mugunta ce kuka yi mini, amma Allah ya maishe ta alheri, don a rayar da jama'a masu yawa waɗanda suke da rai a yau.


An rigyasaninsa a kan haka, tun ba a halicci duniya ba, amma saboda ku ne aka bayyana shi a zamanin ƙarshe.


Ga shi, mazaunan Urushalima da shugabanninsu ba su gane shi ba, sa'an nan kuma ba su fahimci maganar annabawa da ake karantawa kowace Asabar ba, har suka cika maganar nan ta annabawa, yayin da suka hukunta shi.


Ɗan Mutum zai tafi ne, yadda labarinsa yake a rubuce, duk da haka kaiton mutumin nan da yake ba da Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.”


kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na sa ka uban al'ummai da yawa.” Shi ne kuwa ubanmu a gaban Allah, wannan da ya gaskata, wato mai raya matattu, shi ne kuma mai kiran marasa kasancewa kamar sun kasance.


Allahn kakanninmu ya ta da Yesu, wanda kuka kashe ta wurin kafe shi a jikin gungume.


Dukan mazaunan duniya ba a bakin kome suke a gare shi ba. Yakan yi yadda ya nufa da rundunar sama da mazaunan duniya, Ba mai hana shi, ba kuma mai ce masa, ‘Me kake yi?’


Hasalar mutane ba ta ƙara kome, sai dai ta ƙara maka yabo. Waɗanda suka tsira daga yaƙe-yaƙe za su kiyaye idodinka.


Duk mazaunan duniya kuma, za su yi mata sujada, wato, duk wanda, tun farkon duniya, ba a rubuta sunansa a Littafin Rai na Ɗan Ragon nan da yake Yankakke ba.


Gama waɗansu mutane sun saɗaɗo a cikinku, waɗanda tun zamanin dā aka ƙaddara ga hukuncin nan, marasa bin Allah ne, masu mai da alherin Allah dalilin aikata fajirci, suna kuma ƙin makaɗaicin Ubangijinmu Yesu Almasihu.


su da suke zaɓaɓɓu bisa ga rigyasanin Allah Uba, waɗanda Ruhu kuma ya tsarkake, domin su yi wa Yesu Almasihu biyayya, su kuma tsarkaka da jininsa. Alheri da salama su yawaita a gare ku.


Haka Ubangiji ya ce, shi da ya bayyana waɗannan abubuwa tun zamanin dā.


da kuma yadda manyan firistoci da shugabanninmu suka ba da shi don a yi masa hukuncin kisa, suka kuwa gicciye shi.


Ina dai gaya muku, lalle ne a cika wannan Nassi a kaina cewa, ‘An lasafta shi a cikin masu laifi.’ Gama abin da aka faɗa a kaina, tabbatarsa ta zo.”


A cikin annabawa wane ne kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai Adalcin nan, wanda a yanzu kuka zama maciya amanarsa, da kuma makasansa,


Sai suka ce wa juna, “Kada mu tsaga ta, sai dai mu yi kuri'a a kanta, mu ga wanda zai ci.” Wannan kuwa domin a cika Nassi ne cewa, “Sun raba tufafina a junansu. Taguwata kuwa suka jefa kuria akanta.”


Da kuma, “Dutsen sa tuntuɓe, Da fā na sa faɗuwa.” Sun yi tuntuɓe ne da maganar, don sun ƙi biyayya da ita. Haka kuwa aka ƙaddaro musu.


“Ba ka taɓa sani, na riga na shirya a yi haka tuntuni ba? Yanzu ne kuwa na cika wannan. Ni na ba ka iko ka ragargaza birane masu kagarai su zama tsibin ɓuraguzai.


su bashe shi ga al'ummai, su yi masa ba'a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma za a tashe shi.”


Da suka gicciye shi, suka rarraba tufafinsa a junansu ta jefa kuri'a.


Sa'an nan suka gicciye shi, suka rarraba tufafinsa a junansu, suna kuri'a a kansu, su ga abin da kowa zai samu.


Da suka isa wurin da ake ce da shi Ƙoƙwan Kai, nan suka gicciye shi, da kuma masu laifin nan, ɗaya a damansa, ɗaya a hagun.


Nan suka gicciye shi, da kuma waɗansu mutum biyu tare da shi, ɗaya ta kowane gefe, Yesu kuwa a tsakiya.


“Don haka sai duk jama'ar Isra'ila su sakankance, cewa shi Yesun na da kuka gicciye, Allah ya mai da shi Ubangiji, da kuma Almasihu.”


ya ce, “Mun fa kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa da sunan nan, amma ga shi, kun gama Urushalima da koyarwarku, har ma kuna nema ku ɗafa mana alhakin jinin mutumin nan.”


Ɗaukacin waɗanda suka yi zunubi a rashin sanin Shari'a, za su hallaka ne ba tare da Shari'a ba. Ɗaukacin waɗanda suka yi zunubi a ƙarƙashin Shari'a kuwa, za a hukunta su ta hanyar Shari'a.


waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa, suka kuma kore mu, ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuma da dukan mutane,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ