Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 2:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Hakika, har ma a kwanakin nan zan zubo Ruhuna a kan bayina mata da maza, Za su kuma yi annabci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Kai, har ma a kan bayina, maza da mata, zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki, za su kuwa yi annabci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 2:18
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A nan kam, ba hanyar nuna bambanci a tsakanin Ba'al'umme da Bayahude, ko mai kaciya da marar kaciya, ko bare da baubawa, ko ɗa da bawa, sai dai Almasihu shi ne kome, shi kuma yake cikinmu duka.


Ba sauran cewa Bayahude ko Ba'al'umme, ko ɗa, ko bawa, ko namiji ko mace. Ai, dukkanku ɗaya kuke, na Almasihu Yesu.


To, muna nan zaune 'yan kwanaki, sai wani annabi, mai suna Agabas, ya zo daga Yahudiya.


In kuwa bawan nan ya ce a ransa, ‘Ubangijina ya jinkirta zuwansa,’ sa'an nan ya soma dūkan barori, maza da mata, ya shiga ci da sha har yana buguwa,


“ ‘Allah ya ce, A zamanin karshe zai zamanto zan zubo wa dukan 'yan adam Ruhuna. 'Ya'yanku mata da maza za su yi annabci, Wahayi zai zo wa samarinku, Dattawanku kuma za su yi mafarkai.


Zan nuna abubuwan al'ajabi a sararin sama, Da mu'ujizai a nan ƙasa, Wato jini, da wuta, da kuma, hauhawan hayaƙi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ