Ayyukan Manzanni 19:27 - Littafi Mai Tsarki27 Ga shi kuma, akwai hatsari, ba wai cinikinmu kawai ne zai zama wulakantacce ba, har ma haikalin nan na uwargijiya Artimas mai girma zai zama ba a bakin kome ba, har kuma a raba ta da darajarta, ita da duk ƙasar Asiya, kai, har duniya ma duka suke bauta wa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202027 Akwai hatsari, ba kawai cewa sana’armu za tă rasa sunanta mai daraja ba, amma za a yi banza da ɗakin tsafin Artemis alliyarmu mai girma, alliyar kanta wadda ake bauta a ko’ina a yankin Asiya da kuma duniya, za a raba ta da darajarta.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |