sa'an nan kuma Allah ya haɗa shaidarsa, da tasu a kan ceton, ta alamu da abubuwan al'ajabi da mu'ujizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa.
Har Saminu da kansa ma ya ba da gaskiya, bayan an yi masa baftisma kuma ya manne wa Filibus. Ganin kuma ana yin mu'ujizai da manyan al'ajibai, ya yi mamaki ƙwarai.
Haka ta dinga yi kwana da kwanaki, har Bulus ya ji haushi ƙwarai, ya juya ya ce wa aljanin, “Na umarce ka da sunan Yesu Almasihu, ka rabu da ita.” Nan take kuwa ya rabu da ita.
Wato, shi da yake yi muku baiwar Ruhu, yake kuma yin mu'ujizai a cikinku, saboda kuna bin Shari'a ne yake yin haka, ko kuwa saboda gaskatawa da maganar da kuka ji?
Sai duk taron mutane suka yi tsit, suka saurari Barnaba da Bulus, sa'ad da suke ba da labarin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi, da Allah ya yi ga al'ummai ta wurinsu.
Sai Bulus da Barnaba suka daɗe a nan ƙwarai, suna wa'azi gabagaɗi bisa ga ikon Ubangiji, shi da ya shaida maganar alherinsa ta yarjin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi ta hannunsu.
“Lalle hakika, ina gaya muku, duk wanda yake gaskatawa da ni ayyukan da nake yi shi ma haka zai yi. Har ma, zai yi ayyukan da suka fi waɗannan, domin zan tafi wurin Uba.