Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 19:1 - Littafi Mai Tsarki

1 To, lokacin da Afolos yake Koranti, Bulus ya zazzaga ƙasar ta kan tudu, ya gangara zuwa Afisa. A can ya tarar da waɗansu masu bi,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Lokacin da Afollos yake a Korint, Bulus ya bi hanyar da ta ratsa ta Asiya ya zo Afisa. A can ya sadu da waɗansu almajirai,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 19:1
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ga zancen ɗan'uwanmu Afolos kuwa, na roƙe shi ƙwarai, don yă zo wurinku, tare da saurar 'yan'uwa, amma ko kusa bai yi nufin zuwa a yanzu ba. Zai zo dai sa'ad da ya ga ya dace.


Abin da nake nufi, shi ne kowannenku yana faɗar abu dabam, “Ni na Bulus ne,” wani kuwa, “Ni na Afolos ne,” wani kuwa, “Ni na Kefas ne,” ko kuwa, “ni na Almasihu ne.”


Bayan haka Bulus ya tashi daga Atina ya tafi Koranti.


Sai Kirisbus, shugaban majami'ar ya ba da gaskiya ga Ubangiji, shi da jama'ar gidansa duka. Korantiyawa kuma da yawa da suka ji maganar Bulus suka ba da gaskiya, aka kuwa yi musu baftisma.


Wannan abu fa ya sanu ga dukan mazaunan Afisa, Yahudawa da al'ummai duka, duka kuma tsoro ya kama su, aka kuwa ɗaukaka sunan Ubangiji Yesu.


Kuna kuwa ji, kuna gani, ba a nan Afisa kawai ba, kusan ma a duk ƙasar Asiya, Bulus ɗin nan ya rinjayi mutane masu yawan gaske, ya juyar da su, yana cewa, allolin da mutum ya ƙera ba alloli ba ne.


Dā ma kuwa Bulus ya ƙudura zai wuce Afisa cikin jirgin, don kada ya yi jinkiri a Asiya, domin yana sauri, in mai yiwuwa ne ma, ya kai Urushalima a ranar Fentikos.


Da suka zo wurinsa sai ya ce musu, “Ku da kanku kun san irin zaman da na yi a cikinku, tun ran da na sa ƙafata a ƙasar Asiya,


Don dā ma can sun ga Tarofimas Ba'afise tare da shi a cikin gari, sun kuma zaci Bulus ya kawo shi Haikalin.


To, 'yan'uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afolos saboda ku, don ku yi koyi da mu, cewa, kada ku zarce abin da yake a rubuce, kada kuma waninku ya yi fahariya da wani a kan wani.


Idan bisa ga ra'ayin mutum ne, na yi kokawa da namomin jeji a Afisa, mece ce ribata in dai har ba a ta da matattu? “Ba sai mu yi ta ci da sha ba, da yake gobe za mu mutu?”


Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, zuwa ga mutanensa tsarkaka da suke a Afisa, amintattu a cikin Almasihu Yesu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ