Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 18:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Da ya sauka a Kaisariya, sai ya je Urushalima, ya gaisa da Ikkilisiya, sa'an nan ya tafi Antakiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Sa’ad da ya sauka a Kaisariya, sai ya haura ya gai da ikkilisiya sa’an nan ya gangara zuwa Antiyok.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 18:22
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma aka ga Filibus a Azotus. Sai ya zaga dukan garuruwa, yana yin bishara, har ya isa Kaisariya.


Festas kuwa don neman farin jini wurin Yahudawa, ya amsa ya ce wa Bulus, “Ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari'a a can a kan waɗannan abubuwa a gabana?”


To, da Festas ya iso lardinsa, bayan kwana uku sai ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urushalima.


Sa'an nan ya kira jarumi biyu ya ce, “Ku shirya soja metan, da barade saba'in, da 'yan māsu metan, su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan.”


Bulus da Barnaba kuwa suka dakata a Antakiya, suna koyarwa suna kuma yin bisharar Maganar Ubangiji, tare da waɗansu ma da yawa.


Su kuma da aka sallame su, suka tafi Antakiya, da suka tara jama'ar, suka ba da wasiƙar.


da wannan takarda cewa, “Daga 'yan'uwanku, manzanni da dattawan Ikkilisiya, zuwa ga 'yan'uwanmu na al'ummai a Antakiya da ƙasar Suriya da ta Kilikiya. Gaisuwa mai yawa.


Da suka isa Urushalima, Ikkilisiya, da manzanni, da dattawan Ikkilisiya suka yi musu maraba, su kuma suka gaggaya musu dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu.


Daga nan kuma suka shiga jirgin ruwa sai Antakiya, inda tun dā aka yi musu addu'a alherin Allah ya kiyaye su cikin aikin nan da yanzu suka gama.


To, a Ikkilisiyar da take Antakiya akwai waɗansu annabawa, da masu koyarwa, wato Barnaba, da Saminu wanda ake kira Baƙi, da Lukiyas Bakurane, da Manayan wanda aka goya tare da sarki Hirudus, da kuma Shawulu.


Ba zato sai ga mutum uku tsaye a ƙofar gidan da muke, an aiko su wurina ne daga Kaisariya.


Kashegari kuma suka shiga Kaisariya. Dā ma Karniliyas na tsammaninsu, har ya gayyato 'yan'uwansa da aminansa.


An yi wani mutum a Kaisariya, mai suna Karniliyas, wani jarumi ne na ƙungiyar soja da ake kira Ƙungiyar Italiya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ