Ga zancen ɗan'uwanmu Afolos kuwa, na roƙe shi ƙwarai, don yă zo wurinku, tare da saurar 'yan'uwa, amma ko kusa bai yi nufin zuwa a yanzu ba. Zai zo dai sa'ad da ya ga ya dace.
Dā ma kuwa Bulus ya ƙudura zai wuce Afisa cikin jirgin, don kada ya yi jinkiri a Asiya, domin yana sauri, in mai yiwuwa ne ma, ya kai Urushalima a ranar Fentikos.