Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 18:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Can ya tarar da wani Bayahude mai suna Akila, asalinsa kuwa mutumin Fantas ne, bai daɗe da zuwa daga ƙasar Italiya ba, tare da mata tasa Bilkisu, don wai Kalaudiyas ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya je wurinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 A can ya sadu da wani mutumin Yahuda mai suna Akwila, ɗan garin Fontus, wanda ya je can ba da daɗewa ba daga Italiya tare da matarsa Firiskila, gama Kalaudiyus ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya tafi yă gan su,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 18:2
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka gayar mini da Bilkisu da Akila, da mutanen gidan Onisifaras.


Ikilisiyoyin ƙasar Asiya suna gaishe ku. Akila da Bilkisu, tare da ikkilisiyar da take taruwa a gidansu, suna gaishe ku da kyau da kyau saboda Ubangiji.


Sai ya fara wa'azi gabagaɗi a majami'a, amma da Bilkisu da Akila suka ji maganarsa, suka ja shi a jika, suka ƙara bayyana masa tafarkin Allah sosai da sosai.


Sai ɗaya daga cikinsu, mai suna Agabas, ya miƙe tsaye, ya yi faɗi da ikon Ruhu, cewa za a yi wata babbar yunwa, a duniya duka, an yi ta kuwa a zamanin Kalaudiyas.


Bulus kuwa da ya ƙara kwanaki da yawa, bayan ya sausaye kansa a Kankiriya don ya cika wa'adin da ya ɗauka, ya yi bankwana da 'yan'uwa, ya shiga jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, tare da Bilikisu da Akila.


Ga mu kuwa, Fartiyawa, da Madayanawa, da Elamawa, da mutanen ƙasar Bagadaza, da na Yahudiya, da na Kafadokiya, da na Fantas, da na Asiya,


Daga Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zaɓaɓɓun Allah da suke bare, a warwatse a Fantas, da Galatiya, da Kafadokiya, da Asiya, da kuma Bitiniya,


Da aka shirya mu tashin jirgin ruwa zuwa ƙasar Italiya, sai suka danƙa Bulus da waɗansu 'yan sarƙa a hannun wani jarumi, mai suna Yuliyas, na ƙungiyar Augustas.


A nan jarumin ya sami wani jirgin Iskandariya mai zuwa ƙasar Italiya, ya sa mu a ciki.


Ku gai da dukan shugabanninku, da kuma dukan tsarkaka. Waɗanda suke daga ƙasar Italiya suna gaishe ku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ