zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, wato, su waɗanda aka keɓe a cikin Almasihu Yesu, tsarkaka kirayayyu, tare da dukan waɗanda a ko'ina suke addu'a, da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangijinsu da namu duka.
Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, da kuma ɗan'uwanmu Timoti, zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Koranti, tare da dukan tsarkaka na duk ƙasar Akaya.
Waɗanda suka rako Bulus kuwa, sai da suka kai shi har Atina. Bayan Bulus ya yi musu saƙon umarni zuwa wurin Sila da Timoti, cewa su zo wurinsa da gaggawa, suka tafi.
Sai Kirisbus, shugaban majami'ar ya ba da gaskiya ga Ubangiji, shi da jama'ar gidansa duka. Korantiyawa kuma da yawa da suka ji maganar Bulus suka ba da gaskiya, aka kuwa yi musu baftisma.