Ayyukan Manzanni 17:28 - Littafi Mai Tsarki28 Domin “ ‘Ta gare shi ne muke rayuwa, muke motsi, muka kuma kasance,’ kamar yadda waɗansu mawaƙanku ma suka ce, ‘Hakika, mu ma zuriya tasa ce.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202028 ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.