Ayyukan Manzanni 17:17 - Littafi Mai Tsarki17 A kowace rana ya yi ta muhawwara a cikin majami'a da Yahudawa, da waɗansu masu ibada, da kuma waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202017 Saboda haka ya yi ta muhawwara a majami’a da Yahudawa da kuma Hellenawa masu tsoron Allah, haka kuma da waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka ina cike da fushin Ubangiji Na gaji da kannewa. Ubangiji ya ce, “Zan kwararo fushi kan yara da suke a titi. Da kuma kan tattaruwar samari. Za a ɗauke mata da miji duka biyu, Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufa tukub-tukub. Za a ba waɗansu gidajensu, da gonakinsu, da matansu, Gama zan nuna ikona in hukunta mazaunan ƙasar.