Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 16:31 - Littafi Mai Tsarki

31 Su kuwa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 Suka amsa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 16:31
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah,


Wanda ya gaskata da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ya ƙi bin Ɗan kuwa, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah ya tabbata a gare shi.”


Duk wanda ya ba da gaskiya, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma wanda ya ƙi ba da gaskiya za a hukunta shi.


Domin dukanku 'ya'yan Allah ne, ta wurin bangaskiya ga Almasihu Yesu.


Sai Kirisbus, shugaban majami'ar ya ba da gaskiya ga Ubangiji, shi da jama'ar gidansa duka. Korantiyawa kuma da yawa da suka ji maganar Bulus suka ba da gaskiya, aka kuwa yi musu baftisma.


“Ku juyo wurina a cece ku, Ku mutane ko'ina a duniya! Ni kaɗai ne Allah da yake akwai.


“Zan kafa alkawarina da kai, da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu, madawwamin alkawari ke nan, in zama Allahnka da na zuriyarka a bayanka.


Amma Nassi ya kulle kowa a cikin zunubi, don albarkar da aka yi alkawari saboda gaskatawa da Yesu Almasihu, a ba da ita ga masu ba da gaskiya.


Amma mun gaskata, cewa, albarkacin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”


Ba kuma samun ceto ga wani, domin ba wani suna duk duniyan nan da aka bayar cikin mutane, wanda lalle ta wurinsa ne za mu sami ceto.”


Sa'an nan suka gaya masa Maganar Ubangiji, shi da iyalinsa duka.


Lalle hakika ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwami.


Gama nufin Ubana, shi ne duk wanda yake duban Ɗan, yake kuma gaskatawa da shi, yă sami rai madawwani, ni kuma zan tashe shi a ranar ƙarshe.”


Zan ba su zuciya ɗaya, da tafarki ɗaya domin su yi tsorona har abada, domin amfanin kansu da na 'ya'yansu a bayansu.


An yi wannan kuwa domin albarkar nan da aka yi wa Ibrahim ta saukar wa al'ummai ta wurin Almasihu Yesu, mu kuma ta hanyar bangaskiya mu sami Ruhun nan da aka yi alkawari.


Da aka yi mata baftisma tare da jama'ar gidanta, ta roƙe mu ta ce, “Da yake kun amince ni mai ba da gaskiya ga Ubangiji ce, to, sai ku zo gidana ku sauka.” Sai ta rinjaye mu.


Amma an rubuta waɗannan ne, domin ku ba da gaskiya Yesu shi ne Almasihu, Ɗan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai a cikin sunansa.


Wanda zuciyarsa ba daidai take ba, zai fāɗi, Amma adali zai rayu bisa ga bangaskiyarsa.


Gama na zaɓe shi don ya umarci 'ya'yansa da gidansa domin su kiyaye tafarkin Ubangiji a bayansa, su riƙe adalci da shari'a.” Ubangiji ya tabbatar wa Ibrahim da abin da ya alkawarta masa.


In curin farko tsattsarka ne, haka sauran gurasar ma. In kuma saiwa tsattsarka ce, haka rassan ma.


Suna cikin tafiya, suka iso wani ruwa, sai bābān ya ce, “Ka ga ruwa! Me zai hana a yi mini baftisma?”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ