Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 16:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Da aka bulale su da gaske, aka jefa su kurkuku, aka umarci yari ya tsare su da kyau.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Bayan an yi musu bulala sosai, sai aka jefa su cikin kurkuku, aka umarci mai gadin kurkukun yă tsare su da kyau.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 16:23
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.


wadda nake shan wuya saboda ita, har nake ɗaure kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a ɗaure take ba.


duk da haka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu,


Don haka, ni ɗan sarƙa saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi zaman da ya cancanci kiran da aka yi muku,


Domin haka, ni Bulus, ɗan sarƙa saboda Almasihu Yesu domin amfanin ku al'ummai,


Yari kuwa ya shaida wa Bulus maganar, ya ce, “Alƙalai sun aiko a sake ku, saboda haka yanzu sai ku fito, ku tafi lafiya.”


Da yāri ya farka daga barci ya ga ƙofofin kurkuku a buɗe, ya zaro takobinsa, yana shirin kashe kansa, cewa yake 'yan sarƙa sun gudu.


Da gari ya waye kuwa ba ƙaramar rigima ce ta tashi tsakanin sojan nan ba, kan abin da ya sami Bitrus.


Da ya kama shi, ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, su yi tsaronsa, da niyyar kawo shi a gaban jama'a bayan idin.


ya roƙe shi ya yi masa wasiƙu zuwa majami'un Dimashƙu, don in ya sami masu bin wannan hanya, mata ko maza, yă zo da su birnin Urushalima a ɗaure.


Amma Shawulu ya yi ta yi wa Ikkilisiya ɓarna ƙwarai da gaske, yana shiga gida gida, yana jan mata da maza, yana jefa su a kurkuku.


“Mun iske kurkukun a kulle sosai, masu tsaro kuma na tsaro a bakin ƙofofin, amma da muka buɗe, sai muka tarar ba kowa a ciki.”


Amma kafin wannan duka, za su kama ku, su tsananta muku. Za su miƙa ku ga majami'u da kurkuku, su kuma kai ku a gaban sarakuna da mahukunta saboda sunana.


To, mai bashe shi ɗin ya riga ya ƙulla da su cewa, “Wanda zan yi wa sumba, shi ne mutumin. Ku kama shi.”


Ni ne Yahaya, ɗan'uwanku abokin tarayyarku a cikin tsanani, da mulki, da jimiri da suke a cikin Yesu. Ina a can tsibirin da ake kira Batamusa saboda Maganar Allah da kuma shaidar Yesu.


da shan dūka, da shan ɗauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rasa barci, da kuma rasa abinci.


In su bayin Almasihu ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan ɗauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri iri.


Sai Joshuwa ya umarci firistocin su fito daga cikin Urdun.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ