Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 16:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Da suka kai su gaban alƙalai suka ce, “Mutanen nan suna birkita garinmu ƙwarai da gaske, Yahudawa ne kuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Sai suka kawo su a gaban alƙalai suka ce, “Waɗannan Yahudawa ne, suna kuma birkitar mana da gari,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 16:20
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Maciya amana! Ashe, ba ku sani abuta da duniya gāba ce da Allah ba? Saboda haka, duk mai son abuta da duniya, yā mai da kansa mai gāba da Allah ke nan.


Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.


Amma muna so mu ji daga bakinka abin da yake ra'ayinka, don in dai ta ɗariƙar nan ne, mun sani ko'ina ana kushenta.”


amma da suka fahimci, cewa shi Bayahude ne, suka ɗaga murya gaba ɗaya har wajen sa'a biyu, suna cewa, “Girma yā tabbata ga Artimas ta Afisawa!”


Can ya tarar da wani Bayahude mai suna Akila, asalinsa kuwa mutumin Fantas ne, bai daɗe da zuwa daga ƙasar Italiya ba, tare da mata tasa Bilkisu, don wai Kalaudiyas ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya je wurinsu.


Da sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu ƙwarai, haka kuma dukan mutanen Urushalima.


Sarakunan suka ce wa sarki, “A kashe mutumin nan, gama yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran jama'a duka ta wurin irin maganganun da yake faɗa musu. Gama wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan jama'a sai dai wahala yake nemar musu.”


Da iyayengijinta suka ga hanyar samunsu ta toshe, suka danƙe Bulus da Sila, suka ja su har zuwa bakin kasuwa gaban mahukunta.


Suna kuma koyar da al'adun da bai halatta mu karɓa ko mu bi ba, da yake mu Romawa ne.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ