Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 16:12 - Littafi Mai Tsarki

12 daga nan kuma sai Filibi ta ƙasar Makidoniya, wadda take babbar alkarya ce a wannan waje, birnin Romawa ne kuma. A nan birnin muka yi 'yan kwanaki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Daga can muka tafi Filibbi, wata babbar alkaryar Roma wadda kuma take babban birni a gundumar Makidoniya. Muka zauna a can kwanaki masu yawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 16:12
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma ko da yake dā ma can mun sha wuya, an kuma wulakanta mu a Filibi, kamar yadda kuka sani, duk da haka da taimakon Allahnmu muka sanar da ku bisharar Allah gabagaɗi, amma sai da matsanancin fama.


Daga Bulus da Timoti, bayin Almasihu Yesu, zuwa ga dukan tsarkaka a cikin Almasihu Yesu waɗanda suke a Filibi, tare da masu kula da ikkilisiya da kuma masu hidimarta.


Mu kuwa muka tashi daga Filibi a jirgin ruwa, bayan idin abinci marar yisti, muka iske su a Taruwasa bayan kwana biyar. Nan muka zauna har kwana bakwai.


Suna kuma koyar da al'adun da bai halatta mu karɓa ko mu bi ba, da yake mu Romawa ne.”


Wata rana da daddare aka yi wa Bulus wahayi, ya ga wani mutumin ƙasar Makidoniya na tsaye, yana roƙonsa yana cewa, “Ka ƙetaro Makidoniya, ka taimake mu mana.”


Da kuwa ya ga wahayin, nan take sai muka nemi tafiya Makidoniya, muka tabbata cewa Allah ne ya kira mu mu yi musu bishara.


Sa'ad da Sila da Timoti suka zo daga Makidoniya, Bulus ya dukufa a kan yin wa'azi, yana tabbatar wa Yahudawa, cewa Almasihu dai Yesu ne.


Bayan waɗannan al'amura Bulus ya ƙudura a ransa, cewa in ya zazzaga ƙasar Makidoniya da ta Akaya, za shi Urushalima, ya kuma ce, “Bayan na je can, lalle ne kuma in je in ga birnin Roma.”


Sai garin duk ya ruɗe, jama'a suka ruga zuwa dandali da nufi ɗaya, suna jan Gayus da Aristarkus, mutanen Makidoniya, abokan tafiyar Bulus.


Bayan hargowar nan ta kwanta, Bulus ya kira masu bi, bayan ya ƙarfafa musu zuciya, ya yi bankwana da su, ya tafi ƙasar Makidoniya.


ya yi wata uku a nan. Da Yahudawa suka ƙulla masa makirci, a sa'ad da zai tashi a jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, ya yi niyyar komawa ta ƙasar Makidoniya.


Da muka shiga wani jirgi na Adaramitiya, mai shirin tashi zuwa waɗansu garuruwan da suke gaɓar Asiya, muka fara tafiya. Aristarkus kuwa, wani mutumin Tasalonika ta ƙasar Makidoniya, na tare da mu.


Mutanen Makidoniya da na Akaya, sun ji daɗin yin gudunmawar daidai gwargwado ga matalauta, a cikin tsarkakan da suke a Urushalima.


Ina godiya saboda tarayyarku da ni wajen yaɗa bishara, tun daga ranar farko har ya zuwa yanzu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ