Ku yi wa shugabanninku biyayya, ku bi umarnansu, don su ne masu kula da rayukanku, su ne kuma za su yi lissafin aikinsu, don su yi haka da farin ciki, ba da baƙin ciki ba, don in sun yi da baƙin ciki ba zai amfane ku ba.
Da suka isa Urushalima, Ikkilisiya, da manzanni, da dattawan Ikkilisiya suka yi musu maraba, su kuma suka gaggaya musu dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu.
A kan wannan magana kuwa ba ƙaramar gardama da muhawwara Bulus da Barnaba suka sha yi da mutanen ba. Sai aka sa Bulus da Barnaba da kuma waɗansunsu, su je Urushalima gun manzanni da dattawan Ikkilisiya a kan wannan magana.
Sai manzanni da dattawan Ikkilisiya, tare da dukan 'yan Ikkilisiya, suka ga ya kyautu su zaɓi waɗansu daga cikinsu, su aike su Antakiya tare da Bulus da Barnaba. Sai suka aiki Yahuza, wanda ake kira Barsaba, da kuma Sila, shugabanni ne cikin 'yan'uwa,
Lokacin da suke tafiya suna bin gari gari, suka riƙa gaya wa jama'a ƙa'idodin da manzanni da dattawan Ikkilisiya suka ƙulla a Urushalima, don su kiyaye su.