da wannan takarda cewa, “Daga 'yan'uwanku, manzanni da dattawan Ikkilisiya, zuwa ga 'yan'uwanmu na al'ummai a Antakiya da ƙasar Suriya da ta Kilikiya. Gaisuwa mai yawa.
Sa'an nan waɗansu na majami'ar da ake kira majami'ar Libartinawa, wato Kuraniyawa da Iskandariyawa, da kuma waɗansu daga ƙasar Kilikiya da ta Asiya, suka tasar wa Istifanas da muhawwara.
Bulus kuwa da ya ƙara kwanaki da yawa, bayan ya sausaye kansa a Kankiriya don ya cika wa'adin da ya ɗauka, ya yi bankwana da 'yan'uwa, ya shiga jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, tare da Bilikisu da Akila.
Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.