Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 15:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa al'ummai waɗanda suke juyowa ga Allah,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 “Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa Al’ummai waɗanda suke juyowa ga Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 15:19
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin Ruhu Mai Tsarki ya ga ya kyautu, mu ma mun gani, kada a ɗora muku wani nauyi fiye da na waɗannan abubuwa da suke wajibi, wato


Domin su da kansu suke ba da labarin irin ziyartarku da muka yi, da kuma yadda kuka rabu da gumaka, kuka juyo ga Allah, domin ku bauta wa Allah Rayayye na gaskiya,


Tun da muka sami labari, cewa waɗansu daga cikinmu sun ta da hankalinku da maganganu, suna ruɗa ku, ko da yake ba mu umarce su da haka ba,


Da fari, na yi wa mutanen Dimashƙu wa'azi, sa'an nan na yi a Urushalima da dukan kewayen ƙasar Yahudiya, sa'an nan kuma na yi wa al'ummai, cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi aikin da zai nuna tubarsu.


Ku komo wurin Ubangiji, ku roƙe shi, Ku ce, “Ka gafarta mana zunubanmu, Ka karɓe mu saboda alherinka, Mu kuwa za mu yabe ka da bakinmu.


Bari mugaye su bar irin al'amuransu, Su sāke irin tunaninsu. Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu, Shi mai jinƙai ne, mai saurin gafartawa.


Maganar nan ta tashi saboda 'yan'uwan ƙaryar nan ne, da aka shigo da su a asirce, waɗanda suka saɗaɗo su yi ganganen 'yancinmu da muke da shi ta wurin Almasihu Yesu, don dai su sa mu bauta.


Saboda haka, don me kuke gwada Allah, ta ɗora wa almajiran nan kayan da mu, duk da kakanninmu, muka kasa ɗauka?


An kuwa sha gaya musu labarinka, cewa kai ne kake koya wa dukan Yahudawan da suke cikin al'ummai su yar da Shari'ar Musa. Wai kuma kana ce musu kada su yi wa 'ya'yansu kaciya, ko kuwa su bi al'adu.


Amma game da al'ummai da suka ba da gaskiya, mun aika da wasiƙa a kan mun hukunta, cewa su guji cin abin da aka yanka wa gunki, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin nama tare da jini.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ