Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 15:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sai kuma waɗansu mutane suka zo daga Yahudiya suna koya wa 'yan'uwa, suna cewa, “In ba an yi muku kaciya kamar yadda al'adar Musa take ba, ba dama ku sami ceto.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa ’yan’uwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga al’ada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 15:1
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.


Amma waɗansu masu ba da gaskiya, 'yan ɗariƙar Farisiyawa, suka miƙe, suka ce, “Wajibi ne a yi musu kaciya, a kuma umarce su, su bi Shari'ar Musa.”


Ku lura fa, kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa ga al'adar mutane kawai, wato, bisa ga al'adun duniyar nan, ba bisa ga koyarwar Almasihu ba.


A kan rana ta takwas za a yi wa jaririn kaciya.


Tun da muka sami labari, cewa waɗansu daga cikinmu sun ta da hankalinku da maganganu, suna ruɗa ku, ko da yake ba mu umarce su da haka ba,


Musa ya bar muku kaciya, (ba ko shi ya fara ba, tun kakannin kakanni ne), ga shi kuma, kukan yi wa mutum kaciya ko a ran Asabar ma.


Bayan shekara goma sha huɗu na sāke komawa Urushalima tare da Barnaba, na kuma ɗauki Titus.


To, da Ikkilisiya ta raka su, suka zazzaga ƙasar Finikiya da ta Samariya, suna ba da labarin tubar al'ummai, sun kuwa ƙayatar da dukan 'yan'uwa ƙwarai.


don mun ji shi yana cewa wai wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan, yă kuma sauya al'adun da Musa ya bar mana.”


Saboda haka, kada ku damu in wani ya zarge ku a kan abin da kuke ci, ko abin da kuke sha, ko kuwa kan rashin kiyayewar wani idi, ko tsayawar wata, ko Asabar.


Su kuwa da suka ji haka, suka ɗaukaka Allah. Suka ce wa Bulus, “To, kā gani ɗan'uwa, dubban mutane sun ba da gaskiya a cikin Yahudawa, dukansu kuwa masu himma ne wajen bin Shari'a.


Sai manzanni da dattawan Ikkilisiya, tare da dukan 'yan Ikkilisiya, suka ga ya kyautu su zaɓi waɗansu daga cikinsu, su aike su Antakiya tare da Bulus da Barnaba. Sai suka aiki Yahuza, wanda ake kira Barsaba, da kuma Sila, shugabanni ne cikin 'yan'uwa,


To, a kwanakin nan Bitrus ya miƙe tsaye cikin 'yan'uwa, (wajen mutum ɗari da ashirin ne a taron), ya ce,


da wannan takarda cewa, “Daga 'yan'uwanku, manzanni da dattawan Ikkilisiya, zuwa ga 'yan'uwanmu na al'ummai a Antakiya da ƙasar Suriya da ta Kilikiya. Gaisuwa mai yawa.


Yahuza da Sila kuma, da yake su annabawa ne, suka gargaɗi 'yan'uwa da maganganu masu yawa, suka kuma ƙarfafa su.


To, mutanen nan masu son nuna bijinta cikin jiki, su ne masu son tilasta muku yin kaciya, don gudun shan wuya saboda gicciyen Almasihu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ