Lalle zaman da kuka yi na dā, irin wanda al'ummai suke son yi, ya isa haka nan, wato zaman fajirci, da mugayen sha'awace-sha'awace, da buguwa, da shashanci, da shaye-shaye, da kuma bautar gumaka, abar ƙyama.
Ku kuma tuna a lokacin nan a rabe kuke da Almasihu, bare ne ga jama'ar Isra'ila, bāƙi ne ga alkawaran nan da Allah ya yi, marasa bege, marasa Allah kuma a duniya.
Allah kuwa ya ayyana Yesu Almasihu ya zama hadayar sulhu, ta wurin ba da gaskiya ga jininsa. Allah kuwa ya yi haka domin yă nuna adalcinsa ne, domin dā saboda haƙurinsa ya jingine zunuban da aka gabatar,