Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 14:1 - Littafi Mai Tsarki

1 To, a Ikoniya suka shiga majami'ar Yahudawa tare, suka yi wa'azi, har mutane masu yawa, Yahudawa da al'ummai, suka ba da gaskiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A Ikoniyum Bulus da Barnabas suka shiga majami’ar Yahudawa yadda suka saba. A can suka yi magana gabagadi har Yahudawa da Al’ummai masu yawa suka gaskata.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 14:1
33 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya kuma yi ta yin muhawwara a majami'a a kowace Asabar, yana ta rinjayar Yahudawa da al'ummai.


Su kuwa suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaida a kansu, suka tafi Ikoniya.


Sai Bulus da Barnaba suka yi magana gabagaɗi, suka ce, “Ku, ya wajaba a fara yi wa Maganar Allah, amma da yake kun ture ta, kun nuna ba ku cancanci samun rai madawwami ba, to, za mu juya ga al'ummai.


Bayan sun yi bishara a wannan gari, sun kuma sami masu bi da yawa, suka koma Listira da Ikoniya, da kuma Antakiya,


Ba sauran cewa Bayahude ko Ba'al'umme, ko ɗa, ko bawa, ko namiji ko mace. Ai, dukkanku ɗaya kuke, na Almasihu Yesu.


Ai, ba wani bambanci a tsakanin Bayahude da Ba'al'umme. Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa, mayalwacin baiwa ne kuma ga dukkan masu addu'a a gare shi.


Gama ba na jin kunyar bishara, domin ita ce ikon Allah mai kai kowane mai ba da gaskiya ga samun ceto, Yahudawa da fari, sa'an nan kuma al'ummai.


Wannan abu fa ya sanu ga dukan mazaunan Afisa, Yahudawa da al'ummai duka, duka kuma tsoro ya kama su, aka kuwa ɗaukaka sunan Ubangiji Yesu.


Sai ya shiga majami'a yana wa'azi gabagaɗi, ya kuma yi wata uku yana muhawwara da su, yana kuma rinjayarsu a kan al'amarin Mulkin Allah.


Sai Kirisbus, shugaban majami'ar ya ba da gaskiya ga Ubangiji, shi da jama'ar gidansa duka. Korantiyawa kuma da yawa da suka ji maganar Bulus suka ba da gaskiya, aka kuwa yi musu baftisma.


Saboda haka da yawa daga cikinsu suka ba da gaskiya, har da waɗansu Helenawa ba kaɗan ba, mata masu daraja, da kuma maza.


Sai waɗansunsu suka amince, suka koma wajen Bulus da Sila, haka kuma babban taron Helenawa masu ibada, da manyan mata ba kaɗan ba.


Da jama'a suka watse, Yahudawa da yawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci, masu ibada, suka bi Bulus da Barnaba. Su kuma suka yi musu magana, suna yi musu gargaɗi su zauna a cikin alherin Allah.


Ikon Ubangiji kuwa na tare da su, har mutane da yawa da suka ba da gaskiya suka juyo ga Ubangiji.


Nan da nan ya fara wa'azin Yesu a majami'unsu, cewa shi ne Ɗan Allah.


suna ihu suna cewa, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, ku taimaka! Ga mutumin da yake bi ko'ina yana koya wa mutane su raina jama'armu da Shari'a, da kuma wannan wuri. Banda haka kuma har ma ya kawo al'ummai a cikin Haikalin, ya ƙazantar da wurin nan tsattsarka.”


ina tabbatar wa Yahudawa da al'ummai duka sosai wajibcin tuba ga Allah, da kuma gaskatawa da Ubangijinmu Yesu.


A kowace rana ya yi ta muhawwara a cikin majami'a da Yahudawa, da waɗansu masu ibada, da kuma waɗanda yake tararwa a bakin kasuwa.


Sai kuma Bulus ya zo Darba da Listira. Akwai wani almajiri a Listira, mai suna Timoti, ɗan wata Bayahudiya mai bi, ubansa kuwa Bahelene ne.


Amma Yahudawa da suka ƙi bi, suka zuga al'ummai, suka ɓata tsakaninsu da 'yan'uwa.


Da suka kai Salamis, suka sanar da Maganar Allah a majami'un Yahudawa, ga kuma Yahaya na taimakonsu.


To, a cikin waɗanda suka zo idin yin sujada akwai waɗansu Helenawa.


Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina za shi da har ba za mu same shi ba? Za shi wurin Yahudawan da suka warwatsu a cikin al'ummai ne, ya koya wa al'umman?


A nan kam, ba hanyar nuna bambanci a tsakanin Ba'al'umme da Bayahude, ko mai kaciya da marar kaciya, ko bare da baubawa, ko ɗa da bawa, sai dai Almasihu shi ne kome, shi kuma yake cikinmu duka.


Kai, ko Titus ma da yake a tare da ni, ba a tilasta masa yin kaciya ba, ko da yake shi Bahelene ne.


Shekara biyu ana wannan, har dukan mazaunan ƙasar Asiya suka ji Maganar Ubangiji, Yahudawa da al'ummai duka.


Matar kuwa Baheleniya ce, asalinta kuma Basurofinikiya ce. Sai ta roƙe shi ya fitar wa 'ya tata da aljanin.


suna yabon Allah, suna da farin jini a wurin dukan mutane. Kowace rana kuma Ubangiji yana ƙara masu waɗanda ake ceta.


Amma waɗansu Yahudawa suka zo daga Antakiya da Ikoniya, da suka rarrashi taron, suka jejjefe Bulus suka ja shi bayan gari, suna zato ya mutu.


Shi kuwa 'yan'uwan da suke Listira da Ikoniya na yabonsa.


da kuma yawan tsanani, da wuyar da na sha, da suka same ni a Antakiya, da Ikoniya, da Listira, wato irin tsanance-tsanancen da na jure. Amma Ubangiji ya kuɓutar da ni daga cikinsu duka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ