Kuna kuwa ji, kuna gani, ba a nan Afisa kawai ba, kusan ma a duk ƙasar Asiya, Bulus ɗin nan ya rinjayi mutane masu yawan gaske, ya juyar da su, yana cewa, allolin da mutum ya ƙera ba alloli ba ne.
Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, yawan masu bi kuma a birnin Urushalima sai ta ƙaruwa yake yi ƙwarai da gaske, firistoci masu yawan gaske kuma suka yi na'am da bangaskiyar nan.