Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 13:41 - Littafi Mai Tsarki

41 ‘Ga shi, ku masu rainako, Za ku ruɗe don mamaki, ku shuɗe! Domin zan yi wani aiki a zamaninku, Aikin da ba yadda za a yi ku gaskata, Ko da wani ya gaya muku.’ ”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

41 “ ‘Ku duba, ku masu ba’a, ku yi mamaki, ku hallaka, gama zan yi wani abu a zamaninku da ba za ku taɓa gaskatawa ba ko da wani ya gaya muku.’”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 13:41
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya ce, “Ka duba cikin al'umman duniya! Ka gani! Ka yi al'ajabi! Ka yi mamaki! Gama zan yi aiki a kwanakinka, Ko an faɗa maka ba za ka gaskata ba.


Don lokaci ya yi da za a fara shari'a ta kan jama'ar Allah. In kuwa ta kanmu za a fara, to, me zai zama ƙarshen waɗanda ba su bi bisharar Allah ba?


Sa'an nan za ku ce, “Me ya sa ban taɓa koyo ba? Me ya sa ban yarda wani ya kwaɓe ni ba?


suna hana mu yi wa al'ummai wa'azi, don kada su sami ceto. Ta haka a kullum suke cika mudun zunubansu. Amma fa fushin Allah ya aukar musu.


Domin haka ubangiji ya umarce mu, ya ce, “ ‘Na sa ka haske ga al'ummai, Don ka zama sanadin ceto, har ya zuwa iyakar duniya.’ ”


Sai ya ce mini, ‘Tashi ka tafi, zan aike ka can nesa a wurin al'ummai.’ ”


Farisiyawa kuwa da yake masu son kuɗi ne, da jin haka, suka yi masa tsaki.


Zaɓaɓɓun mutane ne za su mori sunayenku wajen la'antarwa. Ni, Ubangiji, zan kashe ku. Amma zan ba da sabon suna ga waɗanda suke yi mini biyayya.


Don haka, kamar yadda tattaka da busasshiyar ciyawa sukan yanƙwane su ƙone a wuta, saiwoyinku za su ruɓe, furanninku kuma za su bushe. Iska za ta kwashe su, domin kun ƙi abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya koya muku.


Zai zamana kuma duk wanda ya ƙi sauraron annabin nan, za a hallaka shi daga cikin jama'a.’


don mun ji shi yana cewa wai wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan, yă kuma sauya al'adun da Musa ya bar mana.”


Mutane da suke tsaitsaye, suna kallo. Shugabanni kuma suka yi masa ba'a, suka ce, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa mana, in shi ne Almasihu na Allah zaɓaɓɓensa!”


Amma idan ka faɗakar da mugu don ya juyo, ya bar muguwar hanyarsa, idan bai juyo ya bar muguwar hanyarsa ba, zai mutu saboda laifinsa, amma za ka tsira da ranka.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ