Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 13:31 - Littafi Mai Tsarki

31 Kwanaki da yawa kuwa yana bayyana ga waɗanda suka zo tare da shi Urushalima daga Galili, waɗanda a yanzu su ne shaidunsa ga jama'a.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 kuma kwanaki da yawa waɗanda suka yi tafiya tare da shi daga Galili zuwa Urushalima suka gan shi. Su ne yanzu shaidu ga mutanenmu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 13:31
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya bayyana kansa gare su a raye bayan shan wuya tasa, tare da tabbatarwa masu yawa, masu ƙarfi kuma, yana bayyana gare su a kai a kai har kwana arba'in, yana zancen al'amuran Mulkin Allah.


Sai suka ce, “Ya ku mutanen Galili, don me kuke tsaye kuna duban sama? Yesun nan da aka ɗauke daga gare ku aka kai shi Sama, zai komo ne ta yadda kuka ga tafiyarsa zuwa Sama.”


Amma za ku sami iko sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”


To, almajirai goma sha ɗayan nan suka tafi ƙasar Galili, suka je dutsen da Yesu ya umarce su.


ba ga dukan jama'a ba, sai dai ga shaidun nan da Allah ya zaɓa tun dā, wato mu ke nan, da muka ci muka sha tare da shi, bayan ya tashi daga matattu.


Mu kuwa shaidu ne ga duk abin da ya yi a ƙasar Yahudawa da Urushalima. Shi ne kuma suka kashe ta wurin kafa shi a jikin gungume.


Mu kuwa shaidu ne ga waɗannan al'amura, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya bai wa masu yi masa biyayya.”


kuka kuwa kashe Tushen Rai, amma Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa shaidu ne ga haka.


Yesun nan kam, Allah ya tashe shi daga matattu, mu kuwa duk shaidu ne ga haka.


tun daga baftismar da Yahaya ya yi, har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi daga wurinmu aka kai shi zuwa Sama, wato ɗaya daga cikin mutanen nan ya zama shaidar tashinsa daga matattu, tare da mu.”


Ku ma shaidu ne, domin tun farko kuke tare da ni.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ