tun da yake ya tsai da ranar da zai yi wa duniya shari'a, shari'a adalci, ta wurin mutumin nan da ya sa, wannan kuwa ya tabbatar wa dukan mutane, da ya tashe shi daga matattu.”
Allah mai zartar da salama, wanda ya ta da Ubangijinmu Yesu, Makiyayin tumaki mai girma, daga matattu, albarkacin jinin nan na tabbatar madawwamin alkawari,
to, sai ku sani, ku duka, da kuma duk jama'ar Isra'ila, da sunan Yesu Almasihu Banazare, wanda ku kuka gicciye, wanda kuma Allah ya tashi shi daga matattu, albarkacinsa ne mutumin nan yake tsaye a gabanku lafiyayye.
Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, Allahn kakanninmu, shi ya ɗaukaka Baransa Yesu, wanda kuka bashe shi, kuka kuma ƙi shi, a gaban Bilatus, sa'ad da ya ƙudura zai sake shi.
Game da ta da shi daga matattu da Allah ya yi, a kan cewa ba zai sāke komawa cikin halin ruɓa ba kuwa, ga abin da ya ce, ‘Zan yi muku tsattsarkar albarkar nan da na tabbatar wa Dawuda.’