“Tuna fa, kada ku manta da yadda kuka sa Ubangiji Allahnku ya yi fushi a jeji. Tun daga ranar da kuka fita daga Masar har kuka iso wannan wuri kuna ta tayar wa Ubangiji.
dukan mutanen da suka ga ɗaukakata da alamuna waɗanda na aikata a Masar, da kuma a jejin, suka kuwa jarraba ni har sau goma, ba su kuma yi biyayya da maganata ba,
“Ka yi haƙuri da su shekaru da yawa, ka gargaɗe su, Annabawanka sun yi musu magana, amma sun toshe kunne. Saboda haka ka sa waɗansu al'ummai su mallaki jama'arka.