Ayyukan Manzanni 12:7 - Littafi Mai Tsarki7 sai ga mala'ikan Ubangiji tsaye kusa da shi, wani haske kuma ya haskaka ɗakin, sa'an nan mala'ikan ya bugi Bitrus a kwiɓi, ya tashe shi, ya ce, “Maza, ka tashi.” Sai kuwa sarƙar ta zube daga hannunsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, wanda ya aiko da mala'ikansa, ya ceci bayinsa masu dogara gare shi, waɗanda kuma ba su yarda su bi umarnin sarki ba, amma suka gwammace a ƙone su maimakon su bauta wa gunki, ko su yi masa sujada, sai dai ga Allahnsu kaɗai.