Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, yawan masu bi kuma a birnin Urushalima sai ta ƙaruwa yake yi ƙwarai da gaske, firistoci masu yawan gaske kuma suka yi na'am da bangaskiyar nan.
wato, bisharar da ta zo muku, kamar yadda ta zo wa duniya duka, tana hayayyafa, tana kuma ƙara yaɗuwa, kamar yadda take yi a tsakaninku tun daga ranar da kuka ji, kuka kuma fahimci alherin Allah na hakika.
A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.
Sa'an nan Daniyel ya tafi wurin Ariyok wanda sarki ya sa ya karkashe masu hikima na Babila, ya ce masa, “Kada ka karkashe masu hikima na Babila, ka kai ni gaban sarki, ni kuwa zan yi wa sarki fassarar.”
“Maganata kamar dusar ƙanƙara take, Kamar kuma ruwan sama da yake saukowa domin ya jiƙe duniya. Ba za su kasa sa amfanin gona ya yi girma ba, Sukan ba da iri domin shukawa, da abinci kuma domin a ci.