Aka jejeffe su da duwatsu, an gwada su, aka raba su biyu da zarto, aka sare su da takobi. Sun yi yawo saye da buzun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, da ƙunci, da wulakanci.
Amma Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Kwa iya sha da ƙoƙon da ni zan sha? Ko kwa iya a yi muku baftisma da baftismar da za a yi mini?”
Ya amsa ya ce, “Ya Ubangiji, Allah Mai Runduna, kai kaɗai nake bauta wa kullayaumin. Amma jama'ar Isra'ila sun karya alkawarinka, sun rurrushe bagadanka, sun karkashe annabawanka, ni ne kaɗai na ragu, ga shi kuma, suna nema su kashe ni.”