4 Sai Bitrus ya fara, yana yi musu bayani bi da bi cewa,
4 Bitrus ya fara yin musu bayani dalla-dalla yadda ya faru cewa,
da yake kuma na bi diddigin kowane abu daidai tun farko, ni ma dai na ga ya kyautu in rubuta maka su bi da bi, ya mafifici Tiyofalas,
Da suka iso, suka tara jama'ar Ikkilisiya suka ba da labarin dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu, da kuma yadda ya buɗe wa al'ummai ƙofar bangaskiya.
Amsa magana da tattausan harshe takan kwantar da hasala, amma magana da kakkausan harshe takan kuta fushi.
Ba ya faɗa musu kome sai da misali, amma a keɓe yakan bayyana wa almajiransa kome.