Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 11:30 - Littafi Mai Tsarki

30 Haka kuwa suka yi, suka aika wa dattawan Ikkilisiya ta hannun Barnaba da Shawulu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 Haka kuwa suka yi, suka aika da kyautarsa wa dattawan ikkilisiyar ta hannu Barnabas da Shawulu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 11:30
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Bayan kuma sun zaɓar musu dattawa a kowace Ikkilisiya, game da addu'a da azumi, suka danƙa su ga Ubangiji, wanda dā ma suka gaskata da shi.


Sai Barnaba da Shawulu suka komo daga Urushalima, bayan sun cika aiken da aka yi musu, suka kuma zo da Yahaya wanda ake kira Markus.


In waninku yana rashin lafiya, to, sai ya kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu'a, suna shafa masa mai da sunan Ubangiji.


Wannan shi ya sa na bar ka a Karita, musamman domin ka ƙarasa daidaita al'amuran da suka saura, ka kuma kafa dattawan ikkilisiya a kowane gari, kamar yadda na nushe ka,


Dattawan ikkilisiya da suke a riƙe da al'amura sosai, a girmama su ninkin ba ninkin, tun ba ma waɗanda suke fama da yin wa'azi da koyarwa ba.


Daga Militas ne ya aika Afisa a kira masa dattawan Ikkilisiya.


Lokacin da suke tafiya suna bin gari gari, suka riƙa gaya wa jama'a ƙa'idodin da manzanni da dattawan Ikkilisiya suka ƙulla a Urushalima, don su kiyaye su.


Sai manzannin da dattawan Ikkilisiya suka taru su duba maganar.


Da suka isa Urushalima, Ikkilisiya, da manzanni, da dattawan Ikkilisiya suka yi musu maraba, su kuma suka gaggaya musu dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu.


Don haka, ku dattawan ikkilisiya da suke cikinku, ni da nike dattijon ikkilisiya, ɗan'uwanku, mashaidin shan wuyar Almasihu, mai samun rabo kuma a cikin ɗaukakar da za a bayyana, ina yi muku gargaɗi,


Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya, da 'ya'yanta waɗanda nake ƙauna da gaske, ba kuwa ni kaɗai ba, har ma dukan waɗanda suka san gaskiya,


Kada ka yarda in an kawo ƙarar wani dattijon ikkilisiya, sai dai da shaidu biyu ko uku.


Kashegari Bulus ya tafi tare da mu wurin Yakubu, dattawan Ikkilisiya kuwa duk suna nan.


da wannan takarda cewa, “Daga 'yan'uwanku, manzanni da dattawan Ikkilisiya, zuwa ga 'yan'uwanmu na al'ummai a Antakiya da ƙasar Suriya da ta Kilikiya. Gaisuwa mai yawa.


A kan wannan magana kuwa ba ƙaramar gardama da muhawwara Bulus da Barnaba suka sha yi da mutanen ba. Sai aka sa Bulus da Barnaba da kuma waɗansunsu, su je Urushalima gun manzanni da dattawan Ikkilisiya a kan wannan magana.


Ana cikin haka sai Yusufu, wani Balawiye, asalinsa mutumin tsibirin Kubrus, wanda manzannin suke kira Barnaba, (wato ɗan ƙarfafa zuciya),


A lokacin nan kuwa sarki Hirudus ya fara gwada wa waɗansu 'yan Ikkilisiya tasku,


Kada ka shagala da baiwar da aka yi maka, wadda aka ba ka ta wurin annabci, sa'ad da dattawan ikkilisiya suka ɗora maka hannu.


Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga Gayus, ƙaunatacce, wanda nake ƙauna da gaske.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ