Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 11:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Ikon Ubangiji kuwa na tare da su, har mutane da yawa da suka ba da gaskiya suka juyo ga Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 11:21
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

suna yabon Allah, suna da farin jini a wurin dukan mutane. Kowace rana kuma Ubangiji yana ƙara masu waɗanda ake ceta.


Duk waɗanda suka ji kuwa suka riƙe a zuciyarsu, suna cewa, “Me ke nan ɗan yaron nan zai zama?” Gama ikon Ubangiji yana tare da shi.


domin bishararmu ba da magana kawai ta zo muku ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma matuƙar tabbatarwa. Kun dai san irin zaman da muka yi a cikinku domin ku amfana,


Duk mutanen Lidda da na ƙasar Sarona kuwa suka gan shi, suka juyo ga Ubangiji.


Duba, ikon Ubangiji bai kasa ba, har da ba zai yi ceto ba. Shi ba kurma ba, har da ba zai ji ba.


domin shi mutum ne nagari cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya. Sai mutane masu yawan gaske suka ƙaru ga Ubangiji.


Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, yawan masu bi kuma a birnin Urushalima sai ta ƙaruwa yake yi ƙwarai da gaske, firistoci masu yawan gaske kuma suka yi na'am da bangaskiyar nan.


Masu ba da gaskiya sai ƙaruwa suke ta yi ga Ubangiji fiye da dā, jama'a masu yawan gaske mata da maza.


Amma da yawa daga cikin waɗanda suka ji wa'azin sun ba da gaskiya, har jimillarsu ta kai wajen mutum dubu biyar.


Wane ne zai gaskata abin da muka ji yanzu? Wane ne zai iya ganin ikon Ubangiji cikin wannan?


Na kuma faɗa musu yadda Allah yana tare da ni, ya kuma taimake ni, da maganar da sarki ya faɗa mini. Sai suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Suka himmatu su yi wannan aiki nagari.


A kuma ba ni takarda zuwa ga Asaf, sarkin daji, domin ya ba ni katakan da zan yi jigajigan ƙofofin kagarar Haikali, da na garun birnin, da na gidan da zan zauna.” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni.


Da yake Allah yana tare da mu, sai suka kawo mana mutum mai ganewa daga 'ya'yan Mali ɗan Lawi, ɗan Isra'ila. Sunan mutumin Sherebiya, da 'ya'yansa da 'yan'uwansa, su goma sha takwas ne.


Suka taso daga Babila a rana ta fari ga watan fari, suka iso Urushalima a rana ta fari ga watan biyar, Allah kuwa yana tare da su.


Ikon Allah kuma yana kan Yahuza, ya ba su zuciya ɗaya ta su yi abin da sarki da sarakunansa suka umarta bisa ga maganar Ubangiji.


Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa al'ummai waɗanda suke juyowa ga Allah,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ