Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 11:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Amma akwai waɗansunsu, mutanen Kubrus da na Kurane a cikinsu waɗanda da isowarsu Antakiya suka yi wa al'ummai magana, suna yi musu bisharar Ubangiji Yesu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Hellenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 11:20
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

To, a Ikkilisiyar da take Antakiya akwai waɗansu annabawa, da masu koyarwa, wato Barnaba, da Saminu wanda ake kira Baƙi, da Lukiyas Bakurane, da Manayan wanda aka goya tare da sarki Hirudus, da kuma Shawulu.


Suna tafiya ke nan, sai suka gamu da wani Bakurane, mai suna Saminu. Shi ne suka tilasta wa ya ɗauki gicciyen Yesu.


Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,


Sa'an nan waɗansu na majami'ar da ake kira majami'ar Libartinawa, wato Kuraniyawa da Iskandariyawa, da kuma waɗansu daga ƙasar Kilikiya da ta Asiya, suka tasar wa Istifanas da muhawwara.


da na Firijiya, da na Bamfiliya, da na Masar, da kuma na kewayen Kurane ta ƙasar Libiya, har ma da baƙi daga Roma, wato Yahudawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci,


Don na ƙudura a raina, sa'ad da nake zaune da ku, ba zan so sanin kome ba, sai dai Yesu Almasihu, shi ma kuwa gicciyeyye.


Har wa yau kuma waɗansu Abikuriyawa da Sitokiyawa masu ilimi suka ci karo da shi. Waɗansu suka ce, “Me wannan mai surutu yake nufi?” Waɗansu kuwa suka ce “Ga alama, mai yin wa'azin bāƙin alloli ne” domin kawai yana yin bisharar Yesu, da kuma tashi daga matattu.


yana wa'azi gabagaɗi da sunan Ubangiji. Ya kuma riƙa magana da Yahudawa masu jin Helenanci, yana muhawwara da su, amma suka yi ta neman kashe shi.


Nan da nan ya fara wa'azin Yesu a majami'unsu, cewa shi ne Ɗan Allah.


Sai Filibus ya buɗe baki ya fara da wannan Nassi, yana yi masa bisharar Yesu.


Filibus ya tafi birnin Samariya, yana ta yi musu wa'azin Almasihu.


Kowace rana kuwa, ko a Haikali ko a gida, ba su daina koyarwa da yin bishara, cewa Yesu shi ne Almasihu ba.


Ana cikin haka sai Yusufu, wani Balawiye, asalinsa mutumin tsibirin Kubrus, wanda manzannin suke kira Barnaba, (wato ɗan ƙarfafa zuciya),


Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina za shi da har ba za mu same shi ba? Za shi wurin Yahudawan da suka warwatsu a cikin al'ummai ne, ya koya wa al'umman?


To, a kwanakin nan da yawan masu bi suke Ƙaruwa, sai Yahudawa masu jin Helenanci suka yi wa Ibraniyawa gunaguni domin bā a kula da matayensu waɗanda mazansu suka mutu, a wajen rabon gudunmawa a kowace rana.


Abin da suka faɗa kuwa ya ƙayatar da jama'a duka. Sai suka zaɓi Istifanas, mutumin da yake cike da bangaskiya da Ruhu Mai Tsarki, da Filibus, da Burokoras, da Nikanar, da Timan, da Barminas, da Nikolas mutumin Antakiya wanda dā ya shiga Yahudanci.


To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin nan da ya tashi kan sha'anin Istifanas, sun yi tafiya har ƙasar Finikiya, da tsibirin Kubrus, da birnin Antakiya, ba su yin wa'azin Maganar Allah ga kowa sai ga Yahudawa kaɗai.


Sai labarin nan ya kai kunnen Ikkilisiyar da take Urushalima, Ikkilisiyar kuma ta aiki Barnaba can Antakiya.


bayan ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antakiya. Shekara sur suna taruwa da Ikkilisiya, suna koya wa mutane masu yawan gaske. A Antakiya ne aka fara kiran masu bi da suna Kirista.


To, a kwanakin nan waɗansu annabawa suka zo Antakiya daga Urushalima.


Daga nan kuma suka shiga jirgin ruwa sai Antakiya, inda tun dā aka yi musu addu'a alherin Allah ya kiyaye su cikin aikin nan da yanzu suka gama.


Sai manzanni da dattawan Ikkilisiya, tare da dukan 'yan Ikkilisiya, suka ga ya kyautu su zaɓi waɗansu daga cikinsu, su aike su Antakiya tare da Bulus da Barnaba. Sai suka aiki Yahuza, wanda ake kira Barsaba, da kuma Sila, shugabanni ne cikin 'yan'uwa,


da wannan takarda cewa, “Daga 'yan'uwanku, manzanni da dattawan Ikkilisiya, zuwa ga 'yan'uwanmu na al'ummai a Antakiya da ƙasar Suriya da ta Kilikiya. Gaisuwa mai yawa.


Su kuma da aka sallame su, suka tafi Antakiya, da suka tara jama'ar, suka ba da wasiƙar.


Da ya sauka a Kaisariya, sai ya je Urushalima, ya gaisa da Ikkilisiya, sa'an nan ya tafi Antakiya.


Amma da Kefas ya zo Antakiya, sai na tsaya masa fuska da fuska don laifinsa a fili yake.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ