Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Bitrus ɗan Yahaya, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki don a faɗar nan ta uku ya ce masa, “Kana sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka, ka kuwa sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina.
Sai Balak ya husata da Bal'amu, ya tafa hannunsa ya ce wa Bal'amu, “Na kirawo ka don ka la'anta maƙiyana, amma ga shi, har sau uku kana sa musu albarka.