Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 10:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Sai Bitrus ya kāda baki ya ce, “Hakika na gane lalle Allah ba ya tara,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 Sa’an nan Bitrus ya fara magana ya ce, “Yanzu na gane yadda gaskiya ne cewa Allah ba ya sonkai

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 10:34
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yanzu fa ku yi tsoron Ubangiji. Ku lura da abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu bai yarda da rashin yin adalci ba, ko son zuciya, ko karɓar rashawa.”


Gama Ubangiji Allahnku, Allahn alloli ne, da Ubangijin iyayengiji. Shi Allah mai girma ne, mai iko, mai bantsoro, wanda ba ya son zuciya, ba ya karɓar hanci.


Mai mugun aiki kuwa za a sāka masa da mugun aikin da ya yi, babu kuma tāra.


Ba ya nuna sonkai ga sarakuna, Ko kuma ya fi kulawa da attajira fiye da matalauta, Gama shi ya halicce su duka.


Da yake kuna kiransa Uba a wajen addu'a, shi da yake yi wa kowa shari'a gwargwadon aikinsa, ba zaɓe, sai ku ƙarasa lokacin baƙuncinku, kuna tsoronsa.


Ku iyayengiji, ku ma ku yi musu haka, ku bar tsorata su, ku sani, shi wanda yake Ubangijinsu da ku duka, yana Sama, shi kuwa ba ya zaɓe.


Suka tambaye shi suka ce, “Malam, ai, mun sani maganarka da koyarwarka duk gaskiya ne. Ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi.


Amma in kun nuna bambanci, kun yi zunubi ke nan, Shari'a kuma ta same ku da laifin keta umarni.


A nan kam, ba hanyar nuna bambanci a tsakanin Ba'al'umme da Bayahude, ko mai kaciya da marar kaciya, ko bare da baubawa, ko ɗa da bawa, sai dai Almasihu shi ne kome, shi kuma yake cikinmu duka.


Waɗanda kuma aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne (ko su wane ne, ai, duk ɗaya ne a guna, domin Allah ba ya tāra), ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙare ni da kome ba.


ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ba ke nan, kuna zartar da hukunci da mugayen tunani?


Kada ku ɓata shari'a, kada ku yi sonzuciya, kada kuma ku karɓi hanci, gama cin hanci yakan makantar da idanun mai hikima, ya karkatar da maganar adali.


Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai.


Sai Filibus ya buɗe baki ya fara da wannan Nassi, yana yi masa bisharar Yesu.


Kada ku nuna bambanci cikin shari'a, ko babban mutum ne ko talaka, duka biyu za ku ji su. Kada ku ji tsoron fuskar mutum, gama shari'a ta Allah ce. In kuwa shari'a ta fi ƙarfinku, sai ku kawo ta wurina, ni kuwa zan yanke ta.’


Nan da nan kuwa na aika maka, ka kuma kyauta da ka zo. To, yanzu ga mu duk mun hallara a gaban Allah, domin mu ji duk irin abin da Ubangiji ya umarce ka.”


Bai kuma nuna wani bambanci tsakaninmu da su ba, tun da yake ya tsarkake zukatansu saboda bangaskiyarsu.


Wato Allah, Allahn Yahudawa ne kurum? Ashe, ba na al'ummai ba ne kuma? Hakika na al'ummai ne ma,


Ya ku 'yan'uwana, kada ku nuna bambanci muddin kuna riƙe da bangaskiyarku ga Ubangijinmu Yesu Almasihu, Ubangiji Maɗaukaki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ