Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 10:1 - Littafi Mai Tsarki

1 An yi wani mutum a Kaisariya, mai suna Karniliyas, wani jarumi ne na ƙungiyar soja da ake kira Ƙungiyar Italiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A Kaisariya akwai wani mutum mai suna Korneliyus, wani jarumin Roma ne, a ƙungiyar soja da ake kira Bataliyar Italiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 10:1
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da aka shirya mu tashin jirgin ruwa zuwa ƙasar Italiya, sai suka danƙa Bulus da waɗansu 'yan sarƙa a hannun wani jarumi, mai suna Yuliyas, na ƙungiyar Augustas.


Sai sojan mai mulki suka kai Yesu cikin fadar mai mulki, suka tara dukan ƙungiyar soja a kansa.


Amma aka ga Filibus a Azotus. Sai ya zaga dukan garuruwa, yana yin bishara, har ya isa Kaisariya.


Amma jarumin da ya so ya ceci Bulus, ya hana i da nufinsu, ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci,


To, da Festas ya iso lardinsa, bayan kwana uku sai ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urushalima.


Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”


sai Bulus ya ce da jarumin yaki da kuma sojan. “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba yadda za a yi ku tsira.”


Bayan 'yan kwanaki sai sarki Agaribas da Barniki, suka zo Kaisariya don su yi wa Festas maraba.


Da baraden suka isa Kaisariya, suka ba mai mulkin wasiƙar, suka kai Bulus a gabansa.


Sa'an nan ya kira jarumi biyu ya ce, “Ku shirya soja metan, da barade saba'in, da 'yan māsu metan, su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan.”


Bayan sun ɗaɗɗaure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa jarumin ɗin da yake tsaye kusa, “Ashe, ya halatta a gare ka ka yi wa mutumin da yake da 'yancin Roma bulala, ba ko bin ba'asi?”


Kashegari muka tashi muka zo Kaisariya, muka shiga gidan Filibus mai yin bishara, wanda yake ɗaya daga cikin bakwai ɗin nan, muka sauka a wurinsa.


Sai ƙungiyar soja da shugabansu, da dogaran nan na Yahudawa suka kama Yesu, suka ɗaure shi,


Yahuza kuwa bayan ya ɗauko ƙungiyar soja, da waɗansu dogaran Haikali daga manyan firistoci da Farisiyawa, suka zo wurin, riƙe da fitilu, da jiniyoyi, da makamai,


To, sai bawan wani jarumi, wanda Ubangijinsa yake jin daɗinsa, ya yi rashin lafiya, har ya kai ga bakin mutuwa.


Sai soja suka tafi da shi cikin fada, wato fadar mai mulkin, suka tara dukkan rundunar soja.


Kashegari kuma suka shiga Kaisariya. Dā ma Karniliyas na tsammaninsu, har ya gayyato 'yan'uwansa da aminansa.


Suna neman kashe shi ke nan, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar yaƙi, wai Urushalima duk ta hargitse.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ