Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 1:5 - Littafi Mai Tsarki

5 domin Yahaya kam, da ruwa ya yi baftisma, amma kafin 'yan kwanaki da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Gama Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma a cikin ’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 1:5
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ni dai, da ruwa nake muku baftisma, shaidar tubarku, amma mai zuwa bayana, ya fi ni girma, wanda ko takalmansa ma ban isa in riƙe ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.


sai Yahaya ya amsa wa dukansu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake yi muku baftisma, amma wani yana zuwa wanda ya fi ni girma, wanda ko maɓallin takalminsa ma ban isa in ɓalle ba. Shi ne zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki, da kuma wuta.


Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda, mu zama jiki guda, Yahudawa ko al'ummai, bayi ko 'ya'ya, dukanmu kuwa an shayar da mu Ruhu guda.


sai ya cece mu, ba don wani aikin adalci da mu muka yi ba, a'a, sai dai domin jinƙan nan nasa, albarkacin wankan nan na sāke haihuwa, da kuma sabuntawar nan ta Ruhu Mai Tsarki,


Ni da ruwa na yi muku baftisma, amma shi da Ruhu Mai Tsarki zai yi muku.”


Bulus ya ce, “Ai, Yahaya baftisma ya yi a tuba, yana faɗa wa mutane su gaskata da mai zuwa bayansa, wato Yesu.”


Sai Yahudawa masu bi, ɗaukacin waɗanda suka zo tare da Bitrus, suka yi mamakin ganin har al'ummai ma an zubo musu baiwar Ruhu Mai Tsarki.


Dā kam, ban san shi ba, sai domin a bayyana shi ga Isra'ila na zo, nake baftisma da ruwa.”


“A wannan lokaci tsaunuka za su rufu da kurangar inabi, Tuddai za su cika da shanu, Dukan rafuffukan Yahuza za su gudano da ruwa, Maɓuɓɓuga za ta gudano daga Haikalin Ubangiji, Ta shayar da kwarin Shittim.


yana yi musu baftisma a Kogin Urdun, suna bayyana zunubansu.


Sai Yahaya ya amsa musu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake baftisma, amma da wani nan tsaye a cikinku wanda ba ku sani ba,


Dā kam, ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ