Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 1:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ya bayyana kansa gare su a raye bayan shan wuya tasa, tare da tabbatarwa masu yawa, masu ƙarfi kuma, yana bayyana gare su a kai a kai har kwana arba'in, yana zancen al'amuran Mulkin Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arba’in ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 1:3
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kwanaki da yawa kuwa yana bayyana ga waɗanda suka zo tare da shi Urushalima daga Galili, waɗanda a yanzu su ne shaidunsa ga jama'a.


Bayan kwana takwas har wa yau almajiransa na cikin gidan, Toma ma yana nan tare da su, ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsaka, ya ce, “Salama alaikun.”


Shi da yake tun fil'azal yake nan, wanda muka ji, muka gani da idonmu, muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa, a game da Kalmar Rai,


Wannan ne fa zuwa na uku da Yesu ya bayyana ga almajiran bayan an tashe shi daga matattu.


Bayan haka Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiran a bakin Tekun Tibariya. Ga kuwa yadda ya bayyana kansa.


Sai kuwa ga Yesu ya tarye su, ya ce, “Salama alaikun!” Suka matso suka rungume ƙafafunsa, suka yi masa sujada.


yana ta wa'azin Mulkin Allah, da koyar da al'amarin Ubangiji Yesu Almasihu gabagaɗi, ba tare da wani hani ba.


ku yi zaman da ya cancanci bautar Allah, wanda yake kiranku ga mulkinsa da ɗaukakarsa.


Ya tsamo mu daga mulkin duhu, ya maishe mu ga mulkin ƙaunataccen Ɗansa,


Ai, Mulkin Allah ba ga al'amarin ci da sha yake ba, sai dai ga adalci, da salama da farin ciki ta wurin Ruhu Mai Tsarki.


“Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al'umma wadda za ta ba da amfani nagari.


Sa'ad da na hau kan dutsen domin in karɓo allunan dutse, wato allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutsen dare arba'in da yini arba'in ban ci ba, ban sha ba.


Da ya yi azumi kwana arba'in ba dare ba rana, daga baya yunwa ta kama shi.


yana cewa, “Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato.”


Sai Iliya ya tashi ya ci abinci ya sha ruwa ya sami ƙarfi, sa'an nan ya kama tafiya kwana arba'in dare da rana har zuwa Horeb, wato dutsen Allah.


Sai na fāɗi ƙasa, na kwanta a gaban Ubangiji dare arba'in da yini arba'in, ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda na yi a dā, saboda dukan zunubin da kuka aikata, kuka yi abin da yake mugu ga Ubangiji, kuka tsokane shi.


To, bayan da Ubangiji Yesu ya yi musu jawabi, aka ɗauke shi aka kai shi Sama, ya zauna dama ga Allah.


Amma da suka gaskata bisharar da Filibus ya yi a kan Mulkin Allah, da kuma sunan Yesu Almasihu, duka aka yi musu baftisma mata da maza.


Sai ya shiga majami'a yana wa'azi gabagaɗi, ya kuma yi wata uku yana muhawwara da su, yana kuma rinjayarsu a kan al'amarin Mulkin Allah.


Da suka sa masa rana, sai suka zo masaukinsa, su da yawa. Sa'an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta shaidar musu Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu a kan Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da littattafan annabawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ