Amma ni ban mai da raina a bakin kome ba, bai kuma dame ni ba, muddin zan iya cikasa tserena da kuma hidimar da na karɓa gun Ubangiji Yesu, in shaidar da bisharar alherin Allah.
Duk sa'ad da nake tare da su, na kiyaye su da ikon sunanka da ka ba ni. Na kāre su, ba kuwa waninsu da ya halaka, sai dai halakakken nan, domin Nassi ya cika.
Kafin ya rufe baki, sai ga taron jama'a suka zo, mutumin da ake kira Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, yake musu jagaba. Sai ya matso kusa da Yesu, don ya sumbace shi.