A lokacin nan muryarsa ta girgiza duniya, amma a yanzu ya yi alkawari cewa, “Har wa yau dai sau ɗaya tak, ba duniya kaɗai zan girgiza ba, amma har sama ma.”
Sa'ad da Ubangiji ya zo domin ya girgiza duniya, jama'a za su ɓuya a cikin kogwannin tuddai da ramummukan duwatsu, suna ƙoƙari su ɓuya daga fushinsa, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa.
Mutane za su ɓuya a kogwannin duwatsu, ko su haƙa ramummuka a ƙasa, suna ƙoƙarin tserewa daga fushin Ubangiji, ko su ɓuya daga ikonsa da ɗaukakarsa, sa'ad da ya zo domin ya girgiza duniya.
Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura, Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki. Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki, Ya ɗora su a wurare masu maƙami. Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne, A kansu ya kafa duniya.