A nan tāke sai aka yi wata babbar rawar ƙasa, sai ushirin garin ya zube, mutum dubu bakwai aka kashe a rawar ƙasar, sauran kuwa suka tsorata, suka ɗaukaka Allah Mai Sama.
Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in dai kuna da bangaskiya, ba tare da wata shakka ba, ba abin da aka yi wa ɓauren nan kaɗai za ku yi ba, har ma in kun ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku,’ sai kuwa ya auku.
Ko da zan yi annabci, ina kuma fahimtar dukkan asiri, da dukkan ilimi, ko da kuma ina da matuƙar bangaskiya, har yadda zan iya kawar da duwatsu, muddin ba ni da ƙauna, to, ni ba kome ba ne.
‘Mene ne kai, ya babban dutse? Za ka zama fili a gaban Zarubabel, zai kuwa kwaso duwatsun da suke ƙwanƙoli da sowa, yana cewa alheri, alheri ne ya kawo haka.’ ”
Ya tsaya, ya auna duniya, Ya duba, sai ya girgiza al'umman duniya. Sa'an nan madawwaman duwatsu suka farfashe, Madawwaman tuddai kuma suka zama bai ɗaya. Haka hanyoyinsa suke tun adun adun.
Akwai wanda zai iya auna teku da tafin hannu, Ko sararin sama da tafin hannunsa? Akwai wanda zai iya tallabe turɓayar duniya a cikin finjali, Ko ya iya auna duwatsu da tuddai a ma'auni?