31 Allah ya jefa ni a kwatami, Har tufafina ma suna jin kunyata.
31 duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri, yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni.
Dukanmu muka cika da zunubi har ayyukanmu mafi kyau ƙazamai ne duka. Saboda zunubanmu, muka zama kamar busassun ganyaye waɗanda iska take faucewa ta tafi da su.
Saƙarku ba za ta yi amfani kamar tufa ba, ba za ku yi sutura da abin da kuka yi ba. Ayyukanku ayyukan mugunta ne, kuna aikata ayyukan kama-karya.
Ba na bukata in kā da kai, Kowace kalma da ka hurta ta kā da ka.
Ni ba ni da laifin kome, amintacce ne ni, A kunne sai a ji kalmomina kamar na marar gaskiya ne. Kowane abu da na fāɗa, kā da ni yake yi.
Ba sabulun da zai iya wanke zunubaina.
Da a ce Allah mutum ne, Da sai in mayar masa da magana, Da sai mun je ɗakin shari'a a yanka mana shari'a.
Ka kuwa ce, ‘Wace riba na ci? Wane fifiko nake da shi fiye da idan na yi zunubi?’
Zan watsa miki ƙazanta, In yi miki wulakanci, In maishe ki abin raini.
Za ka soke zunubaina ka kawar da su, Za ka shafe dukan kurakuran da na taɓa yi.
Ko da za ka yi wanka da sabulun salo, Ka yi amfani da sabulu mai yawa, Duk da haka zan ga tabban zunubanka. Ni Ubangiji Allah na faɗa.