21 Ba ni da laifin kome, amma ba na ƙara damuwa. Na gaji da rayuwa.
21 “Ko da yake ba ni da laifi, ban damu da kaina ba; na rena raina.
Akwai wani mutum a ƙasar Uz, mai suna Ayuba, amintacce ne, mai tsoron Allah. Shi mutumin kirki ne, natsattse, yana ƙin aikata kowace irin mugunta.
Wanda yake dogara ga son zuciyarsa, wawa ne, amma wanda yake tafiya cikin hikima zai kuɓuta.
Ba za ka iya gafarta mini zunubina ba? Ba za ka kawar da kai ga muguntar da na aikata ba? Ba da daɗewa ba zan rasu in koma a ƙura, Lokacin da ka neme ni ba za ka same ni ba.”
duk sa'ad da zuciyarmu ta ba mu laifi, saboda Allah ya fi ta, ya kuma san kome.
Ban sani ina da wani laifi ba, amma ba don wannan na kuɓuta ba, ai, Ubangiji shi ne mai gwada ni.
Da ma ya ci gaba kawai ya kashe ni, Ko ya sake ikonsa ya datse ni!
Ko da yake ba ni da laifi, Duk da haka iyakar abin da zan iya yi ke nan, In roƙi Allah ya yi mini jinƙai, Shi da yake alƙalina.
Ka sani, ba ni da laifi, Ka kuma sani, ba wanda zai cece ni daga gare ka.
Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu, Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi, Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu'o'ina.
A shirye nake in faɗi ƙarata, Domin na sani ina da gaskiya.
Ka ce kai tsattsarka ne, ba ka da laifi, Kai tsabtatacce ne, ba ka da wata ƙazanta.