18 Ya hana ni in ko shaƙata, Ina jin haushin dukan abin da yake yi mini.
18 Ba zai bari in yi numfashi ba, sai dai yă ƙara mini azaba.
Ba za ka ko ɗan kawar da kai ba, Don in samu in haɗiye yau?
Ya shayar da ni da ruwan ɗaci, Ya ƙosar da ni da abinci mai ɗaci.
Ai, kowane irin horo, a lokacin shansa, abu ne mai baƙin ciki, ba na farin ciki ba. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.
Hakika ikonsa ya yi ta gāba da ni dukan yini.
Fushinka yana da nauyi a kaina, An turmushe ni a cikin tuƙuƙinka.
Ka ƙyale ni ko zan sami kwanciyar rai, Kafin in tafi, ai, tawa ta ƙāre.”
“Na rantse da Allah Mai Iko Dukka, Wanda ya ƙwace mini halaliyata, Wanda ya ɓata mini rai.
“Me ya sa ake barin mutane su yi ta zama cikin damuwa? Me ya sa ake ba da haske ga waɗanda suke baƙin ciki?
Raina bai kusa ƙarewa ba? A bar ni kawai! Bari in ci moriyar lokacin da ya rage mini.
Ka kawo mugayen ƙararraki a kaina, Har da laifofin da na yi na ƙuruciya.
Ita kuwa ta ce musu, “Kada ku kira ni Na'omi, wato mai farin ciki, sai dai Mara, wato mai baƙin ciki, gama Mai Iko Dukka ya wahalshe ni ƙwarai.
Amma suka taurare, suka biye wa zuciyarsu, suka bi Ba'al, kamar yadda kakanninsu suka koya musu.