14 To, ƙaƙa zan yi in samo kalmomin da zan amsa wa Allah?
14 “Ta yaya zan iya yin faɗa da shi? Ina zan iya samun kalmomin da zan yi gardama da shi?
“Ka amsa mini, in ka iya, Ka shirya abubuwan da za ka faɗa mini, ka yi tsaye a kansu.
To, mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah?”
Ina da aminci, zan faɗa wa Allah ra'ayina, Zai tabbatar da amincina duka.
Da zan kai ƙarata a gare shi, in faɗa masa duk muhawarata, in kāre kaina ne.
Ta ƙaƙa za ka iya jayayya da shi? Yana yiwuwa ya yi maka tambayoyi guda dubu Waɗanda ba wanda zai iya ba da amsarsu.
Ta ƙaƙa zai amince da talikinsa wanda aka yi da ƙasa, Abin da yake na ƙura, ana kuwa iya murƙushe shi kamar asu.
“Amma ko Allah zai zauna a duniya? Ga shi, Saman sammai ba ta isa ta karɓe ka ba, balle wannan Haikali da na gina!
Da a ce Allah mutum ne, Da sai in mayar masa da magana, Da sai mun je ɗakin shari'a a yanka mana shari'a.
Ka koya mana abin da za mu faɗa masa, Ba za mu iya gabatar da ƙararrakinmu ba, gama mu dolaye ne.